Featured
Kashi 80 Na Matsalolin Tsaro Shaye-Shayen Miyagun Ƙwayoyi Ne Ke Haddasawa – Gwamnan Sokoto

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ne ke haddasa kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta. Ya ce wannan annoba na daga cikin manyan barazanar da ke addabar matasa da ci gaban al’umma.
Gwamnan, wanda mataimakinsa Idris Mohammed Gobir ya wakilta a wani taron wayar da kai kan illar miyagun ƙwayoyi, ya ce yawancin masu aikata laifuka da ’yan bindiga na aikata ta’addanci ne saboda tasirin ƙwayoyi. Ya ƙara da cewa shaye-shaye na lalata rayuwar matasa, iyalai da kuma ƙara yawaitar laifuffuka a cikin al’umma.
Read Also : Ƙudirin Kafa ’Yan Sandan Jihohi Ya Isa Gaban Majalisun Jihohi
Aliyu ya yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin addini da na gargajiya, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa hannu wajen yaƙi da shaye-shaye. Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafa wa shirye-shiryen hana amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma gyaran rayuwar waɗanda abin ya shafa.