Featured
Abdussamad BUA Na Shirin Mallakar Kaso 70% Na Ƙungiyar Kano Pillars

Mutum na uku mafi arziki a Afirka, kuma shugaban kamfanin BUA Group, Abdul Samad Rabiu, ya gabatar da tayin sayen kaso 70 cikin 100 domin mallakar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars daga Gwamnatin Jihar Kano. An ce darajar yarjejeniyar ta kai kusan dala miliyan 1.1.
Wannan mataki ya biyo bayan kiran da Hukumar Shirya Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) ta yi ga ƙungiyoyin da gwamnatoci ke mallaka da su rungumi tsarin haɗin gwiwa da masu zaman kansu, tare da ƙarfafa gwamnatoci su sayar da kaso tsakanin 50 zuwa 75 cikin 100 ga masu zuba jari.
Read Also : NDC Za Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Rajistar Jam’iyyar
Express radio ta bayyana cewa tayin ya biyo bayan wata ganawar sirri tsakanin Abdul Samad Rabiu da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Idan aka amince da yarjejeniyar, Kakaki24 ta ruwaito cewa wannan zai zama babban sauyi a tarihin Kano Pillars, inda a karon farko ƙungiyar za ta koma tsarin mallakar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.