Featured
INEC Ta Ƙara Wa’adin Mika Sunayen ‘Yan Takarar Zaɓen 2027
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙara wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa domin mika sunayen ‘yan takararsu na zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya na shekarar 2027 da ƙarin kwanaki uku.
A wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, INEC ta ce sabon wa’adin zai ƙare da tsakar daren Talata, 14 ga Yulin 2026, maimakon 11 ga Yuli da aka tsara tun farko.
Read Also : The Missing Commissioner: Unravelling The Controversy Behind The Arewa Media Summit
Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan roƙon Ƙungiyar IPAC a madadin jam’iyyun da ba su samu damar loda sunaye da bayanan ‘yan takararsu cikin wa’adin da aka kayyade ba. INEC ta kuma buƙaci jam’iyyun su yi amfani da wannan dama wajen kammala aikin kafin sabon wa’adin ya cika.
