Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarrabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin jarrabawar WAEC da NECO ga ɗaliban sakandire, domin sake nazari da tuntuɓar masu ruwa da tsaki. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta fitar.
Tun da farko, ma’aikatar ta sanar da shirin ƙara kuɗin jarrabawar daga naira 27,000 zuwa naira 50,000 daga shekarar 2027, inda ta danganta matakin da ƙalubalen tattalin arziki da tsadar gudanar da jarrabawar.
Read Also : Gov. Yusuf Nominates Garo as Running Mate for 2027 Re-election Bid
Sai dai matakin ya jawo suka da muhawara daga ƴan ƙasa da dama, waɗanda suka yi gargaɗin cewa hakan na iya ƙara yawan ɗaliban da za su daina karatu. Ma’aikatar ta ce ta yaba da shawarwarin da ta karɓa, wanda ya sa aka dakatar da shirin domin ci gaba da tattaunawa.