Connect with us

Featured

INEC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Sabbin Ma’aikata

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buɗe shafin ɗaukar ma’aikata na shekarar 2026, inda ta gayyaci ‘yan Najeriya da suka cancanta su nemi guraben aiki a matakan albashi na Grade Level 07, 08, 09, 10 da 12. An buɗe shafin neman aikin ranar 20 ga Yuli, kuma za a rufe shi ranar 27 ga Yuli.

Hukumar ta bayyana cewa ɗaukar ma’aikatan na da nufin ƙarfafa ayyukanta a fannonin gudanar da zaɓe, rajistar masu kaɗa ƙuri’a, sarrafa bayanai da kuma gudanar da ayyukan zaɓe. Ta kuma jaddada cewa babu bukatar biyan kudi domin neman aikin.

Read Also : Akanta Janar Ne Ya Bamu Umarnin Buɗe Asusu Ga Hukumar da Ake Zargin Ta Bogi Ce – CBN

INEC ta gargaɗi masu neman aikin da su guji gabatar da bayanan ƙarya ko takardun bogi, tana mai cewa duk wanda aka kama da hakan za a cire sunansa daga tsarin ɗaukar ma’aikatan tare da yi masa hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Masu sha’awar neman aikin za su iya yin rajista ta shafin hukumar na yanar gizo: https://recruitment.inecnigeria.org/⁠�, inda za su cike fom ɗin neman aiki tare da loda takardun da ake buƙata. Hukumar ta ce waɗanda aka tantance ne kawai za a gayyata zuwa mataki na gaba na ɗaukar ma’aikatan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet