Featured
ICPC ta sake gano wasu hukumomin bogi guda biyu

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bayyana cewa ta gano wasu ƙarin hukumomin bogi guda biyu yayin da take ci gaba da bincike kan hukumar Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC).
Shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 06 ga Agusta, bayan miƙa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu rahoton wucin-gadi na binciken a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya ce ana zargin Adeniyi Matthew Adeyemi da ƙirƙirar wasu hukumomin bogin, bayan ya yi amfani da giɓin da ke cikin tsarin wasu hukumomin gwamnati.
Read Also : Yanzu-yanzu : Tinubu ya ba wa EFCC umarnin gaggauta buɗe asusun gwamnatin Osun
Aliyu ya ce binciken ya tabbatar da cewa Adeyemi bai taɓa samun naɗi daga Gwamnatin Tarayya ba, sannan PFIPC ba ta da wata halastacciyar kafa, domin ba a kafa ta ta kowace doka, umarnin shugaban ƙasa ko wata takardar gwamnati ba.
Ya ƙara da cewa an miƙa rahoton ne kwanaki 30 bayan Shugaba Tinubu ya ba ICPC umarnin gudanar da bincike kan PFIPC. Haka kuma ya jaddada cewa abin da ake kira PFIPC ba hukuma ce ta gwamnatin tarayya ba, kuma ba ta taɓa samun sahalewar gudanar da aiki daga gwamnati ba.