Featured
Kotu ta yanke wa Bashar Al-assad hukuncin kisa

Wata kotun Syria ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa kan laifukan da ya aikata a lokacin yaƙin basasar ƙasar.
Kotun Manyan Laifuka da ke Damascus ta same shi da laifin kisan kai da gangan, inda alkalin kotun ya ce Assad ya yi amfani da hukumomin gwamnati wajen aikata laifukan yaƙi da na cin zarafin bil’adama.
An yanke wa Assad hukuncin ne duk da bai halarci kotun ba, yayin da ɗan uwansa Ate Najib, tsohon shugaban tsaron siyasa a lardin Deraa, shi ma aka yanke masa hukuncin kisa kan kisan kai da gangan da azabtarwa.
Wannan shi ne hukunci na farko da kotu ta yanke wa Assad ko wani daga cikin na kusa da shi tun bayan kawo ƙarshen mulkinsa a 2024. Bayan hamɓarar da gwamnatinsa, Assad da ɗan uwansa Maher sun tsere zuwa Rasha, inda suka samu mafaka ta siyasa.