Featured
NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 13
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 tsakanin 11 zuwa 20 ga Agustan 2026.
Jihohin sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna, Nasarawa, Adamawa, Filato, Benue, Kogi, Taraba, Cross River da Akwa Ibom.
Read Also : Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta buƙaci hukumomi a Najeriya su kama Sheikh Jingir
NiMet ta ce hasashen ya samo asali ne daga nazarin yawan ruwan sama da ake sa ran samu, danshin ƙasa, ƙarfin magudanan ruwa, yanayin ƙasa da kuma madatsun ruwa.
Hukumar ta shawarci jama’a su bibiyi hasashen yanayi, su guji hanyoyin da ruwa ya mamaye, tare da buƙatar hukumomin agajin gaggawa da manoma su ɗauki matakan kariya.
