Connect with us

Featured

Obi ya rasa damarsa ta lashe zaben 2027 ne tun ranar da ya fice daga ADC – Fayose

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce Peter Obi ya rasa damar da yake da ita ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 tun ranar da ya fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa Nigeria Democratic Congress (NDC).

Fayose ya bayyana hakan ne a wata hira da TVC News, inda ya ce ficewar Obi da wasu ’yan adawa daga ADC, ta raunana yiwuwar samun haɗin kan ’yan adawa wajen kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Ya ce da suna tare a ADC, da yana ganin za su iya yin tasiri.

Read Also : Najeriya ta samu fiye da Triliyan 15 sakamakon cire tallafin man fetur — Gwamnatin Tarayya 

Sai dai Fayose ya bayyana Obi a matsayin “ɗan Najeriya na kwarai” wanda ya yi fice kuma ya nuna cewa abubuwa na iya inganta. Ya ce amma rashin haɗin kan ’yan adawa zai ci gaba da raunana damarsu, yana mai cewa yanzu ya yi latti a sauya matsayar da aka ɗauka.

Game da damar Bola Tinubu a 2027, Fayose ya ce tsarin siyasa a Kudu maso Yamma a yanzu yana nuna cewa shugaban na da babbar dama, inda ya yi hasashen zai iya samun kusan ƙuri’u miliyan huɗu daga yankin. Ya kuma ce matsalar maguɗin zaɓe abu ce da ta shafi dukkan ɓangarorin siyasa, kuma tana buƙatar haɗin gwiwar ‘yan siyasa da masu zaɓe wajen magance ta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet