Featured
2027: APC Ta Musanta Janye Sunayen Mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu

Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke cewa ta janye jerin sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na 2027 domin sake dubawa. Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Felix Morka ne ya bayyana hakan ga Jaridar TheCable a ranar Talata, ya ce jita-jitar ce kawai, yana mai cewa duk wani sauyi za a sanar da shi a hukumance.
APC ta fitar da jerin kwamitin ne ranar Asabar, inda Tinubu yake matsayin shugaba, Kashim Shettima da Nentawe Yilwatda mataimakan shugaba, yayin da tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari, aka naɗa Darakta-Janar. Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, kuma aka naɗa sakataren kwamitin.
Morka ya ce idan akwai dalilin sabunta jerin sunayen, jam’iyyar za ta sanar da hakan yadda ya kamata. Wannan na zuwa ne bayan rahotannin cewa an fara duba jerin sakamakon koke-koke kan shigar da wasu jami’an gwamnati da kuma mutanen da ake zargin suna da batutuwan cin hanci da rashawa.
Batun ya kuma jawo suka daga ’yan adawa, ciki har da Rabiu Kwankwaso da Dino Melaye, yayin da Ministan Tsaro Christopher Musa da Ministan Ƙasa na Tsaro Bello Matawalle, waɗanda ke cikin kwamitin, suka ce nadin nasu kira ne zuwa ƙarin hidima, tare da tabbatar da cewa ayyukan tsaro za su ci gaba ba tare da tangarda ba.