Featured
Duk matar da mijinta ya hana ta zaɓar APC a 2027 ta kashe auren ta fito – Shugaban APC na Yobe

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Muhammad Gadaka, ya buƙaci matan auren da mazajensu suka hanasu zaɓar APC a zaɓen 2027 su nemi saki, inda ya ce shi zai biya sadakinsu idan za su yi wani auren. Gadaka ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Nangere ranar Alhamis.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa, shugaban APC ɗin ya ce matan da mazajensu ba za su bar su su zaɓi APC ba kawai su kashe auren. Sai dai kalaman nasa sun jawo suka daga wasu mazauna da malaman addinin Musulunci, waɗanda suka bayyana su a matsayin masu tayar da hankali da kuma barazana ga darajar iyali.
Read Also : Gwamnatin Kano ta fitar da iyakoki tsakanin Jam’iar Bayero da alummar Rimin zakara bayan kammala biyan diyya
Daga baya Gadaka ya nemi afuwa tare da janye kalaman nasa. Ya bayyana cewa abin da ya faɗa wasa ne kawai, kuma ba ya wakiltar abin da ya yi imani da shi ko kuma yana nufin ƙarfafa mutane su rabu da aurensu.
Kalaman shugaban APC na Yobe sun zo ne kwanaki kaɗan bayan kwamishinan matasa da wasanni na jihar Borno, Sainna Buba, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya yi barazanar yi wa mutanen da suka ƙi goyon bayan APC bulala a zaɓen 2027.