Featured
Zargin Alaƙa Da ’Yan Bindiga: Sanata Shehu Buba ya miƙa kansa ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike
Sanatan Bauchi ta Kudu, kuma dan takarar gwamnan Bauchi na jam’iyyar PRP a 2027, Shehu Buba Umar, ya ce a shirye yake ya fuskanci cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi masa na alaƙa da ’yan bindiga, ɗaukar nauyin ta’addanci ko garkuwa da mutane. Ya ce da kansa ya miƙa kansa ga DSS domin gudanar da bincike.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Bauchi a ranar Litinin, Sanatan ya musanta zarge-zargen gaba ɗaya, yana mai cewa bai taɓa ɗaukar nauyin ’yan bindiga ko tallafa musu da kuɗi, makamai ko wata hanya ba, ya ce zarge-zargen ba sababbi ba ne, domin an yaɗa irin wadannan maganganu tun shekarar 2014, amma binciken da aka gudanar a wancan lokacin ya karyata zarge-zargen. Ya kuma ce kamata yayi duk wanda ke da hujja ya mika ta ga hukumomin da suka dace, ba cece-kuce a kafafen sada zumunta ba.
Read Also Gwamnatin Sokoto ta rufe masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa
Buba ya ce tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Yakubu Chonoko Maikyau, SAN, ta rubuta wa DSS, DIA da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya buƙatar gudanar da cikakken bincike.
Sanatan ya ce ya amince a gurfanar da shi a kotu kuma a hukunta shi idan bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu a laifukan da ake zarginsa da su.
