Featured
Kudin hajji na iya ƙaruwa saboda sabbin sauye-sauyen Saudiyya – NAHCON

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta ce kuɗin aikin Hajjin na iya ƙaruwa sakamakon sabbin manufofin da Masarautar Saudiyya ke shirin aiwatarwa. A halin yanzu, kuɗin Hajjin 2027 yana tsakanin Naira miliyan 7.5 da miliyan 7.8, gwargwadon wurin da mahajjaci zai sauka.
Shugaban NAHCON, Ambasada Isma’il Yusuf, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai ranar Litinin, inda ya ce farashin na iya sauyawa cikin shekaru uku masu zuwa. Ya ce Saudiyya na shirin soke tsarin kunshin Grade D, wanda mahajjatan Najeriya ke amfani da shi wajen samun ragi a kuɗin aikin Hajji.
Read Also : An yanke wa matashi hukuncin shekara guda a gidan gyaran hali kan satar tumatir
Ya ce Saudiyya na kuma shirin rage mahajjatan da gwamnati ke kula da su zuwa kashi biyu cikin 100, yayin da kamfanonin yawon buɗe ido za su kula da kashi 98 cikin 100. Ya ce shirin da aka tsara fara aiwatar da shi a bana an dage shi zuwa shekaru uku masu zuwa sakamakon ƙoƙarin diflomasiyya da hukumar ta yi.
Shugaban NAHCON ya ce hukumar za ta ci gaba da taka rawar da ta dace wajen tabbatar da jin daɗin mahajjatan Najeriya. Ya kuma ce suna aiki tare da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi domin sauya tsarin aikinsu zuwa tsarin masu shirya tafiye-tafiye, domin su dace da sabbin sauye-sauyen da Saudiyya ke shirin aiwatarwa.