Featured
Yanzu-yanzu : Kotu ta soke tikitin takarar Pantami

Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta umarci Jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani domin tantance ɗan takararta na gwamnan Jihar Gombe.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar tsayar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Read Also : Yobe Showcase Economic Potential at UNGA 2026 For Strategic Partnerships, Investments
Garry ya ƙalubalanci tsayar da Pantami bayan PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takara tilo a ranar 26 ga Yuni 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani da ya dace ba. Pantami ya koma PDP ne bayan APC ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na yarjejeniya.
Sai dai kotun ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe. A baya, Pantami ya samu tikitin PDP ne ta hanyar amincewa da baki yayin zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayu.