Featured
2027: Peter Obi ya yi watsi da kwamitin yaƙin neman zaɓensa da OK Movement ta kafa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi watsi da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen da ƙungiyar Obi-Kwankwaso Movement (OK Movement) ta kafa domin zaɓen 2027.
Obi ya bayyana cewa NDC ce jam’iyyar siyasar da magoya bayansa suke cikinta, don haka OK Movement, ƙungiyar Obidient da Kwankwasiyya kamata yayi su kasance ƙungiyoyin tallafi ga jam’iyyar, ba su maye gurbin tsarin jam’iyyar ba.
Read Also : Dangote Da Habasha Sun Kulla Yarjejeniyar Gina Bututun Man Fetur Na Dala Miliyan 600
A ranar 17 ga Satumba, OK Movement ta sanar da kafa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe mai mambobi 59, wadda ta ƙunshi masu kula da shiyyoyi da jihohi da kuma daraktoci masu kula da fannoni daban-daban. Sai dai NDC ta bayyana cewa kwamitin bai samo asali daga jam’iyyar ba.
Da yake magana a shirin Prime Time na Arise TV, Obi ya ce bai san da kafa kwamitin ba kuma bai amince da shi ba. Ya ce duk wani abu da OK Movement za ta yi da ya shafi shi da Rabiu Kwankwaso, ya kamata a samu amincewarsu kai tsaye.
Pingback: Mun yi nadamar amincewa da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi - NLC - KAKAKI 24