Featured
Zaɓen 2027: Arewa za ta bai wa Tinubu ƙuri’u fiye da na 2023 — Shettima

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Arewa za ta ƙara yawan ƙuri’un da za ta bai wa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, fiye da kashi 60.2 cikin 100 da ta ba shi a 2023.
Shettima ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ƙungiyar Arewa for Asiwaju, wadda ke goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Read Also : Rundunar ƴan sandan Kano ta yi alkawarin tabbatar da Tsaro yayin zaɓen 2027
Ya buƙaci shugabannin siyasa a yankin su haɗa kai wajen mara wa Shugaba Tinubu baya, yana mai cewa Arewa ta riga ta nuna gamsuwarta da shugabancinsa.
Mataimakin shugaban ya kuma ce yankin ba shi da abin da zai ji tsoro dangane da yunƙurin Tinubu na neman wa’adi na biyu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Pingback: Kano za ta jagoranci Arewacin Najeriya wajen ganin an sake zaɓar Tinubu a 2027 — Abba Kabir Yusuf - KAKAKI 24