Featured
Tambuwal Ya Musanta Jita-jitar Komawa APC

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar, ya bayyana cewa babu wani shiri na komawarsa APC, yace ikirarin da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama.
Read Also : Al’ummar Kano Atiku Za Su Zaɓa
Sanarwar ta ce alaƙar abokantaka da Tambuwal ke da ita da ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, sakamakon shekarun da ya shafe yana aikin gwamnati, hakan ba yana nufin yana shirye-shiryen sauya sheƙa bane. Ta kuma ce hotuna da bidiyoyin da ake yaɗawa ba su tabbatar da hakan ba.
Ofishin ya jaddada cewa Tambuwal na ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ADC, inda hankalinsa ya karkata wajen ƙarfafa jam’iyyar da kuma shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.