Addini
Na yi addu’a ga dukkan ƴan Najeriya a lokacin da nake Ibadar Umara – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da wadata ga daukacin ’yan Najeriya, biyo bayan kammala ziyararsa zuwa Masarautar Saudiyya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X da aka tabbatar. Ya ce ziyarar ta nuna dorewar alakar addini, abota da mutunta juna tsakanin Najeriya da Saudiyya.
Read Also : Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Jam’iyyar ADC
Shugaban ya ce yayin ziyarar, shi da tawagarsa sun samu damar shiga cikin Ka’aba mai alfarma tare da gudanar da Umrah. Tinubu ya kuma bayyana godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mohammed bin Salman bisa wannan dama da kuma kyakkyawar kulawar da aka nuna musu.
Tinubu ya ce a cikin wannan lokaci mai tsarki, ya roki Allah Ya kawo zaman lafiya, hadin kai da wadata ga Najeriya da daukacin ’yan kasar.

Pingback: Tinubu ya karbi shugabancin Najeriya a lokacin da take dab da durƙushewa - Gwamnan Filato - KAKAKI 24