Connect with us

Featured

Zaɓen 2027: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar ɗan takarar gwamnan Kano a NDC zuwa Disamba 

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sake ɗage sauraron ƙarar da ke ƙalubalantar sahihancin takarar jam’iyyar NDC a zaɓen gwamnan jihar Kano na 2027 zuwa ranar 7 ga Disamba, 2026.

Ƙarar mai lamba FHC/KN/CS/440/2026, wadda wasu mambobin NDC guda uku suka shigar, na neman kotu ta hana jam’iyyar tsayar da Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takararta na gwamna, tare da ƙalubalantar sahihancin takararsa da na mataimakinsa, Mustapha Rabiu Kwankwaso.

Read Also : Duk da zage-zagen da wasu ƴan siyasa ke yi har yanzu ƴan Najeriya na tare da APC – Abdulaziz Yari 

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan Gwarzo, Barista Magaji Mato, ya gabatar da ƙin amincewa da ƙarar, yana mai cewa masu shigar da ƙarar ba su da sahihiyar hujjar kasancewarsu mambobin NDC, sannan kuma an shigar da ƙarar ne bayan wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada. Lauyan masu ƙarar ya nemi ƙarin lokaci domin ba da amsa ga ƙin amincewar.

Sai dai kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga Disamba, 2026. Wannan lamarin dai na cigaba da haifar da rashin tabbas kan matsayin takarar NDC a Kano, musamman ganin cewa har yanzu sunayen Gwarzo da mataimakinsa ba su bayyana a jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta wallafa ba.

Share this:
Exit mobile version
meram escortvipcrpytogiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvholiganbet xholiganbetjojobet xjojobet xjojobet xgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbet girişholiganbet girişholiganbet girişpusulabetgrandpashabetjojobetgrandpashabetjojobet girişjojobetjojobetjojobet girişholiganbetcasibomcasibomgrandpashabetjojobet güvenlikjojobet güvenliksekabetholiganbet girişholiganbet girişmarsbahisholiganbetcasibomcasibomholiganbetholiganbet girişmarsbahispusulabetmarsbahis girişmarsbahismarsbahis girişholiganbetcasibomcasibomjojobet erişimgrandpashabetgrandpashabetcasibomnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobetjojobetjojobet