Connect with us

Featured

Ra’ayi: Dalar Shinkafa a Abuja

Ko shakka babu shugaba Buhari ya daura Nigeria akan kyakkyawan tafarki na ta noma abincin da za ta ci, duk da yake yan arewa da su abin zai fi amfana, basu yi maraba da wannan kyakkyawar aniya ta Gwamnatin Buhari ba. A tunanin gwamnatin tana ganin, tunda yake kashi 70 na mutanen kasar sun fi amfani da shinkafa ne, ya sanya ta maida himma wurin noman shinkafar, domin dai tayi amanna da cewa, zanin aro baya rufe katara.

Ni a ganina wannan ba karamin yunkuri bane, inda mutane sun rungumi abin bilhakki. Kuma da gwamnonin jihohin Arewa sun kama abin da gaskiya. Amma kash, sai abin ya zamar mana kishiya mayya, miji barawo, wato dai shege da hauka. Gwamnatin Buhari ta fitar da biliyoyin Naira domin tallafawa manoman shinkafa, amma kuma aka sanya siyasa inda aka ringa karkatar da akalar wadannan kudade zuwa inda ba nan aka nufa fa da su ba. Karshe dai mai doki ya koma kuturi, mai kaza ya tashi da kai da kafa, yan gata suka dau cinya da kirji. Wani babban bala’in da yayi wa wannan kyakkyawar aniya tarnaki shi ne, matsalar tsaro a gonaki da dazuzzuka, inda yan fashin daji ke cin karan su babu babbaka. Wannan ya sanya kusan kashi 40 na kasashen da za su iya noman shinkafar ba su iya nomawa.

To amma duk da haka dai, alkaluma sun nuna Nigeria na kan gaba wurin noman shinkafa a Africa, kuma tana cikin sahun gaba na kasashen duniya da suka fi noma shinkafa. Hakan na nufin in har za a inganta tsaro, a kuma tsaftace tsarin bayar da lamunin noma a Nigeria, nan da 2030 shinkafa kan iya kafada da kafada da man fetur wurin samarwa kasar kudaden shiga koma ta haura shi.

To a jiya kuma sai muka tashi da wasu hotuna da ke zagayawa a kafafen sadarwa na zamani, na wata dalar shinkafa da ake yi akan titin airport na Abuja. Hakan ya jawo cecekuce a tsakanin masu goyon bayan muradan gwamnatin da yan adawar ta. A yayin da yan adawa ke kallon abin da cewa kawai burga ce irin ta gwamnati, su masu goyon baya na kallon wannan wani babban cigaba ne.

A matsayina na mai goyon bayan gwamnati, ina jinjina mata da wannan hobbasa, kuma ina ganin dole ace wa mijin iya Baba. To amma duk da yake ban san me yasa aka yi wannan dala ba, ban kuma san su waye suke yin ta ba, tunda ba lallai bane gwamnati na da hannu a abin. Ina ganin wannan abu ba a sanya kwaryar a gurbin ta ba. Da farko dai, Abuja cibiyar jagoranci ce bata kasuwanci ba, ba kuma ta shahara da noman shinkafa ba, kamata yayi ace a Kano ko Jigawa ko Kebbi aka yi wannan dala. Domin nan ne cibiyar abin.

Na biyu gwamnatin Buhari bata bukatar tayi dalar shinkafa domin ta nunawa duniya daya daga cikin kokarin da tayiwa kasar nan na fidda a’i daga rogo. Da nine zan maida himma ne wurin nuna kamfanonin sarrafa shinkafa da aka kafa sakamakon wannan takidi na habbaka noman shinkafar. Domin sanin kan kowa ne, kafin zuwan gwamnatin Buhari, kamfanonin basu taka kara sun karya ba, a yanzu kuwa a tsakanin Kano da Jigawa kawai, daga kanana zuwa marsakaita zuwa manya sun haura 500. Hakan ya nuna mutane a yanzu suna zuba jarin su a noma da sarrafa shinkafar, sabanin shekarun baya da mutane ke gudun sana’ar.

Fatuhu Mustapha ya rubuto daga birnin tarayyar Nigeria, Abuja

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet