Addini
Sarkin Musulmi Ya Yi Umarnin Da Aduba Jinjirin Watan Zul-hijja Mai Kamawa

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi da su duba jinjirin watan Dhul-Hijja tun daga ranar Laraba.
Abubakar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Sokoto ranar Talata, mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi ta Sokoto.
“Wannan yana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Yuni daidai da 29 ga watan Zul-Qidah 1443AH ita ce ranar da za a duba jinjirin watan Zul-Hijjah na shekarar 1443 bayan hijira.
“Saboda haka, an bukaci Musulmai da su fara neman jinjirin wata ranar Laraba kuma su kai rahoto ga gunduma ko kauye mafi kusa don tuntubar Sarkin Musulmi,” “in ji shi.
Sarkin Musulmi ya roki Allah da ya taimaki al’ummar Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.
Zul-Hijja shi ne wata na 12 a jerin watannin musulinci kuma na karshe a cikin kalandar Musulunci da ake gudanar da aikin Hajji a cikinsa, da kuma gudanar da bikin Sallar idin layya. (NAN)