Connect with us

Labarai

Bai Kamata A Dinga Siyasantar Da Matsalar Rashin Tsaro Ba – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya gargadi shugabannin siyasa da na addini da ma daukacin ‘yan Najeriya game da siyasantar matsalar rashin tsaro a kasar.

Ana samun karuwar ayyukan ta’addanci a yayin da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da sauran al’amura ke ta’azzara ta’addanci a yankin Arewa maso yamma da Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya.

An kashe mutane da dama, an yi garkuwa da wasu domin neman kudin fansa da fyade tare da lalata kadarori da dama, lamarin da ya tilastawa wasu gwamnatocin jihohin rufe harkokin sadarwa a matsayin matakin riga-kafi na dakile ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yamma.

Da yake jawabi a Abuja a wani taron koli na tsaro na bai daya da gidauniyar Global Peace Foundation tare da hadin gwiwar Vision Africa suka shirya, Sultan ya yi nazari kan yanayin tsaron kasar inda ya ce komai bai yi wa al’ummar kasar dadi ba.

“Kada mu sanya siyasa cikin rashin tsaro domin yunwa bata san siyasa addini ba. Kowa ya yi ta korafin yunwa a kasar kuma gaskiya ne,” in ji Sarkin Musulmi.

“Daya daga cikin manyan matsalolin da muka sani shi ne mai yunwa mutum ne mai fushi. Yana da mahimmanci a gare mu, a duk lokacin da muka hadu a matsayin shugabannin addini, na siyasa, dole ne mu kalli abu daya. Mu fara lura da Dan Adam.”

Ya kuma yi Allah-wadai da yawaitar kashe-kashe a kasar, inda ya nemi gwamnati ta samar da yanayi mai kyau ga ‘yan Najeriya don su kiyaye addininsu.

Duk da tabarbarewar rashin tsaro, Abubakar na da kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta iya fuskantar dimbin kalubalen tsaro. Sarkin Musulmi ya yi kira da a ba da hadin kai a tsakanin ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko addini ko kabilanci ba.

Ya ce, “Muna samun mutane suna kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ko dai da sunan addini ko da sunan ‘yan fashin daji, ko ta’addanci ko ma menene. Shi ya sa muke cigaba da yin kira ga dukkanmu da mu koma ga littattafanmu masu tsarki, mu yi aiki da kalmomin Alkur’ani a gare mu Musulmi da kuma Littafi Mai Tsarki ga Kiristoci.

“Abu ne mai mahimmanci a gare mu a koyaushe mu waiwaya baya mu tattauna wasu daga cikin wadannan batutuwa a fili. A Najeriya dole ne mu daina dora laifi. Duk abun da ya faru ya faru kuma zai cigaba da faruwa sai dai idan ba mu taru akalla don magance matsalolin ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet