Ilimi
Yajin Aiki: Kungiyar SSANU, NASU Ta Ki Amincewa Da Rahoton Kwamitin Gwamnatin Tarayya

Rikicin da ake fama da shi a tsarin jami’o’in kasar nan ya dauki sabon salo a yayin da mambobin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU) da kungiyar ma’aikatan jami’o’i (NASU) suka yi watsi da rahoton kwamitin sake tattaunawa da Farfesa Nimi Briggs.
Kungiyoyin biyu sun dage kan cewa ba za su yi aiki da shawarwarin kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin kawo karshen yajin aikin da ke faruwa a jami’o’in kasar nan ba.
Babban Sakataren NASU, Peters Adeyemi, da Shugaban SSANU na kasa, Mohammed Ibrahim, ne suka bayyana matsayin kungiyoyin a ranar Juma’ar nan a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Abuja.
Sun ce ba su taba kammala tattaunawa da kwamitin ba kafin ya mika shawarwarinsa ga gwamnati don aiwatar da shi, suna mai jaddada cewa irin wannan aikin cin amana ne.
A wani yunkuri na warware rikicin da ke faruwa a bangaren jami’o’i, a watan Maris ne gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Briggs domin tattaunawa da NASU da SSANU, da kuma kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Kungiyar ASUU ta dakatar da harkokin ilimi a jami’o’in gwamnati tun ranar 14 ga watan Fabrairu lokacin da malaman suka fara yajin aikin, lamarin da ya daure kai yayin da NASU da SSANU suma suka yi watsi da kayan aikin a watan Afrilu.