Uncategorized
Bankin duniya ya tallafa wa mata da yara 1,097,048 da abinci mai gina jiki

Bankin Duniya, ya tallafa wa mata da ƙananan yara kimanin 1,097,048 da kayayyakin abinci mai gina jiki da na tsaftar jiki a jihar Kaduna.
Babban Jami’in kula da ayyukan kula da lafiyar iyali SFH, a Jihar Kaduna Malam Murtala Ibrahim, ne ya bayyana hakan a fadar mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Bamalli, yayin da suka kai masa ziyara a Larabar makon nan.
Ya ce, shirin bada tallafin bangare ne na tabbatar da samun abinci mai gina jiki na bankin duniya watau ANRIN na shekarar farko da aka aiwatar a jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, a shekarar farko da fara aiwatar da aikin, ya samar da ayyukan cigaban al’umma har guda tara dukkansu ga mata da kananan yara kan batun abinci mai gina jiki da lafiyar matasa.
Malam Murtala Ibrahim, ya kuma ce, shirin SFH na ba da shawarwari kan shayar da jarirai nonon uwa musamman ga mata masu juna biyu da masu shayarwa don ba su damar tallafawa jariransu.