Uncategorized
Bauchi: Hukumar FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane 11 sakamakon hatsarin mota

Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta Najeriya FRSC shiyyar jihar Bauchi, ta ce, mutane goma sha ɗaya sun rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da su.
Kwamandan hukumar Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Lahadi.
Haka kuma ya ƙara da cewa mutane takwas sun samu munanan raunuka a hatsrin.
Ya kuma ce, hatsarin ya afku ne a ƙarshen makon nan a ƙauyen Hawan Jaki dake kan titin Alkaleri zuwa Gombe.
Kwamandan ya alakanta musabbabin hatsarin da tuƙin gudun wuce sa a da direbobin motocin ke yi da suka haɗar da babbar motar ɗaukar kaya da motar fasinjoji ta Ya kari.