Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na jami’ar Lamara Garba, ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta kuma buƙaci ɗalibai da su koma makarantar ba tare da ɓata lokaci ba domin ci gaba da harkokin karatu.
Wannan dai na zuwa ne bayan da ƙungiyar Malaman jami’o’i ASUU ta jingine yajin aikin da take yi na tsawon watanni takwas.
