Labarai
Gwajin Maganin Bindiga: Matashi ya harbe ƙaninsa ya tsere

Rundunar ƴan sandan Jihar Kwara, ta ce, tana ci gaba da neman wani matashi mai suna Abubakar ruwa a jallo bisa zarginsa da harbe ƙaninsa Yusuf ɗan shekera goma sha biyu lokacin da yake gwajin maganin bindiga a kansa.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawunta SP Okasanmi Ajayi, ya fitar.
SP Okasanmi, ya ce, rundunar ta bada umarnin cafko duk mutumin da ke da hannu wajen aikata laifin.
Kafar BBC ta ruwaito cewa lamari ya faru ne a garin Dutse Gogo da ke yankin ƙaramar hukumar Kaiama a Lahadin da ta gabata.
Haka kuma ta ƙara da cewa afkuwar lamarin ya janyo mazauna yankin sun shiga halin firgici da jimami.