Labarai
Zamfara: Sojoji sun hallaka Ƴan bindiga yayin da suke yin noma

Dakarun rundunar Operation Hadarin Daji na sojojin ƙasa da ke yaƙi da ƴan bindiga a jihar sun ce sun kashe ƴan bindiga a ƙauyen Ƴar Tasha na ƙaramar hukumar Maru.
Daraktan yada labarai na na hukumar tsaron kasar Manjo janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Litinin.
Ya ce a lokacin harin dakarun sojin sun kwato babur daya, tare da makamai da wasu kayayyaki daga wajen ‘yan bindigar.
Rahotonni sun ce an kashen ƴan bindigar ne a lokacin da suke girbe kayan amfanin gona da suka shuka a gonakinsu da ke kauyen.