Featured
INEC: Za a fara tattara sakamakon zaɓe a gobe Lahadi
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana cewa za a fara tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a gobe Lahadi.
Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a dakin taro na hukumar INEC da ke cikin cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Abuja.
Shugaban ya ce tsarin tantance masu kaɗa kuri’a na BVAS ya yi aiki yadda ya kamata a yawancin jihohin ƙasar, sai dai hukumar ta fuskanci ƙalubale a wasu sassan zaɓen.
