Labarai
Gini mai hawa 7 ya rufto a Lagos

Wani bene mai hawa 7 da ake tsaka da ginawa a yankin Banana Island da ke Ikoyi a jihar Legas ya rufto.
BBC ta ruwaito cewa, ginin ya rufto ne da tsakar ranar yau Laraba.
Haka kuma ta bayyana cewa, ginin ya rufta ne a lokacin da wasu daga cikin masu aikin ginin suka tashi.
Ta kuma ce, akwai wasu mutane da suka jikkata sakamakon ruftowar ginin.
Rahotonni sun bayyana cewa, mai magana yawun hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Amodu Shakiri ya tabbatar da faruwar al’amari, yana mai cewa ginin ya rubzo ne da misalin ƙarfe 3:58 na yamma.