Uncategorized
Jam’iyyar APC ta buƙaci kotu ta bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓe

Jam’iyyar APC, ta buƙaci hukumar zaɓe INEC, da ta bayyana ɗan takararta na gwamna Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen gwamnan Kano.
Jam’iyyar ta buƙaci hakan ne ta cikin takardar ƙarar lauyoyinta suka shigar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe
A cewar jam’iyyar APC, ɗan takarar jam’iyyar adawa ta NNPP Abba Kabir Yusuf bai cancanci tsayawa takara ba, saboda babu sunansa a cikin jerin mambobin jami’yyar NNPP da aka tura wa hukumar INEC.
Haka kuma APC ta ƙara da cewa, Abba Kabir Yusuf bai ci zaɓe ba, saboda mafi yawa na kuri’un da aka kaɗa masa lalatattu ne.
Haka zalika APC ta ce tazarar kuri’un da Abba Kabir Yusuf ya bai wa Ganduje, adadin kuri’u da aka soke su sun fi su yawa.