Labarai
Alasan Ado Doguwa ya karɓi shaidar lashe zaɓe

Hukumar INEC, ta bai wa Alhassan Ado Doguwa shaidar lashe zaɓen kujerar majalisar wakilai ta mazaɓar Doguwa da Tudun Wada a zaɓen bana.
Hukumar ta damƙa masa shaidar samun nasara a zaɓen ne da tsakar ranar yau Laraba.
Wannan dai shi ne karo na biyar da Alhassan Ado Doguwa, ke wakiltar yankunan a zauren majalisar tarayya tun bayan dawowar Najeriya tsarin mulki Dimukuraɗiyya.
Ba shi shaidar dai ta biyo bayan nasarar da ɗan majalisar ya samu a zaɓen da aka gudanar a zagaye na biyu ranar 16 ga wannan watan da muke ciki na Afrilu.