Uncategorized
Hukumar FAAN Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Tasi A Filin Jirgin Sama

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN ta sanar da dakatar da ayyukan motocin haya a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ba tare da bata lokaci ba.
A cikin wata sanarwa da Abdullahi Yakubu-Funtua ya sanyawa hannu, yace an yi wannan dakatarwar ne saboda rashin warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin ma’aikatan motocin haya da ke shafar ayyukan motocin haya da ke cikin filin jirgin.
“Sakamakon wannan dakatarwar, Hukumar FAAN ta shawarci jama’a da duk masu amfani da filin jirgin, musamman ma fasinjojinmu da su yi amfani da wasu amintattun hanyoyin sufuri ko kuma wayar da kan jama’a a ciki da wajen filin jirgin.
“Hukumar FAAN ta yi nadamar duk wata matsala da wannan dakatarwar zata iya haifarwa da fasinjojin mu, masu amfani da filin jirgin da sauran jama’a.
“Ayyukan Hayar Mota na yau da kullun zasu koma dai dai da zarar an warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu,” in ji sanarwar.