Uncategorized
Wani Matashi Yayi Sanadin Rasa Abokinsa Saboda Abinci

Wani mutum mai suna John ya rasa ransa bayan abokinsa, Akinola Adeleye, ya caka masa wuka har lahira a kan takaddamar wanda zai biya kudin farantin abinci.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ifako Ijaiye da ke jihar Legas.
An tattaro cewa mutanen biyu sun samu rashin fahimta kan wanda zai biya kudin farantin abincin da Akinola ya ci, kuma a cikin takaddamar da ta rikide zuwa fada, Akinola ya daba wa John wuka har lahira.
PUNCH Metro ta samu labari daga wasu mazauna yankin cewa lamarin ya faru ne makonni biyu da suka gabata a kan titin Idiagbon daura da shedikwatar karamar hukumar.
An kuma tattaro cewa wanda aka kashen yana tsugunne a gida wanda ake zargin a lokacin da suka samu sabani kan wanda zai biya kudin farantin abinci.
Wani mazaunin yankin mai suna Ugochukwu, wanda ya shaida wa wakilinmu abin da ya faru a ranar Laraba, ya ce, “Abin da ya faru Akinola ya je ya ci farantin guda na abinci a wurin da suka saba, bayan ya ci abinci maimakon ya biya sai ya ce su sa a takardar biyan abokinsa wanda ba ya tare da shi a lokacin.
“Don haka, a lokacin da wanda aka kashe ya je cin abinci a gidan cin abinci na yankin, sai suka sanar da shi cewaya bar bashin abincin da abokinsa ya ci. Ya yi mamaki da fushi ya abokin nasa zai ce su yi haka ba tare da ya gaya masa ba.
“Saboda haka, da sauri ya gama cin abinci ya tafi gida don ya fuskanci abokinsa game da bashin da aka ci masa. A haka suka fara rigima. A yayin da suke fafatawa a kan lamarin, Akinola, cikin fushi ya bukaci John da ya fice masa daga gida nan take, amma John ya ki, kuma fada ya yi tsanani.
“Kafin kowa ya san abin da ke faruwa, Akinola ya bar wurin da ake fadan, ya kuma dawo da wuka ya daba wa John. Mun dauka fada ya kare ne a lokacin da Akinola ya tafi, sai kawai muka ga ya zo da wuka a ya bugawa John.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda ya kara da cewa tuni aka kai wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar.
Ya kuma shaida wa wakilinmu cewa za a gurfanar da shi a kotu ranar Juma’a (yau).
Sufetan ‘yan sandan ya ce, “A gobe ne za a ci gaba da shari’ar.”