Featured
Gwamnan CBN Ya Barranta Kansa Da Alhakin Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasar Nan

Gwamnan babban bankin Kasa CBN, Olayemi Cardoso, ya ce shi da tawagarsa ba su da hannu a tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Olayemi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a wani taron kwamitin kula da harkokin kudi (MPC) na babban bankin, wanda shi ne na farko, tun bayan hawansa kujerar gwamnan CBN a watan Satumban 2023.
Shugaban babban bankin, ya ce CBN na daukar matakan da suka dace don farfado da harkokin kudi da ma kudaden kasar nan yadda ya kamata.