Connect with us

Featured

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Akalla 49 A Zamfara

Akalla mutane 49 ake zargin ‘yan bindiga sun kashe a wani samame na kwanaki biyar a jihar Zamfara.

Lammarin, a cewar mazauna garin, an kashe su ne a wasu kauyuka biyar da lamarin ya shafa a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara daga ranar Talata zuwa Asabar.

A cewar mazauna yankin, an kashe mutane 18 a kauyen Farar-Kasa; 22 a Dangulbi, sai mutum biyu a Duhuwa, hudu kuma a Tsatsomawa da wasu uku a kauyukan Yar Sabaya.

Wani mazaunin garin Anka, Malam Idris Anka (ba sunansa na gaskiya ba kenan) ya ce tun farkon makon nan ne ‘yan bindigar ke kai hare-hare a cikin al’ummomin karamar hukumar.

Ya ce, “’Yan bindiga sun zama ruwan dare a wannan yanki na Jihar Zamfara. Gaskiyar magana, mun gaji da wannan barazanar. ’Yan fashi suna ta aiki kamar ba mu da gwamnati a kasar nan, ‘yan sanda, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.

“Za su iya kai hari ga kowace al’umma yadda suke so, sanya haraji a kan kowace al’ummar da suke so kuma su sace kowa a kowace al’umma kuma ba wanda ke da ikon ya ce komai kan umarnin da suka bayar.”

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da kyar ya tsere wa ‘yan bindigar a kan hanyar Anka zuwa Bagega a ranar Asabar inda ya ce “’yan bindiga biyu sanye da kakin soji sun kafa wani shingen bincike ba bisa ka’ida ba a kan hanyar a jiya suna fashi.

Mallam Bello Muhammad, wani direban ‘yan kasuwa ne, ya roki gwamnatin tarayya da ta jihohi da su kawo musu dauki ta hanyar samar da isassun jami’an tsaro a yankin, domin a cewarsa rashin kasancewar tsaro na taimaka wa ‘yan fashi a kananan hukumomin.

Jaridar Daily Trust ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya yi alkawarin tuntubar jami’in ‘yan sanda mai kula da sashen Anka domin jin cikakken bayani; sai dai bai sake kiranmu ba, ko kuma ya amsa wasu kiraye-kirayen da aka yi masa.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta yi watsi da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na shirin zaman lafiya da ‘yan bindiga a jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet