Featured
Niger: Ƴanbindiga sun sace fasinjoji fiye da 20

Wasu gungun ‘yan bindiga, sun sace fasinjoji fiye da ashirin wadanda ke cikin motoci biyar a kan hanyar Mariga zuwa Kontagora da ke jihar Neja.
Shugaban majalisar dokokin jihar kuma wakilin mazaɓar Mariga Abdulmalik Sarkin-Daji, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai lokacin da yake mayar da martani kan yadda sojojin Najerya suka musanta labarin.
Shugaban majalisar ya ce, wadanda suka sace fasinjojin, sun tare hanyar ne ranar Alhamis a dai-dai titin Babbar Lamba da Beri inda suka yi awon-gaba da matafiyan.
Haka kuma, ya ce, iyalan wadanda aka sace a baya suna kai wa barayin dajin kuɗin fansa sau da dama a cikin dajin, wanda ya ce bangare ne na sansanin atisayen sojoji.
Haka kuma, ya kara da cewa, su ma waɗanda aka sace ranar Alahamis an kai su dajin ne, inda ya yi kira ga hukumomin sojin na Najeriya da su nemi bayanai na gaskiya su je su kawar da waɗannan ɓarayin daji.