Connect with us

Featured

Majalisa Ta Aikewa Tinubu Ƙudurorin Dokar Haraji Domin Ya Rattaba Hannu

Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka.

Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata 18 ga Yuni 2025 a Abuja.

A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar kudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka.

Kudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a fadin kasa, kafin daga bisani majalisun na wakilai da dattawa su amince da su.

Sanata Yemi ya ce, “Eh, yanzu kudurin ya bar hannunmu, yana kan hanyarsa ta zuwa wajen Shugaban Kasa domin ya sanya masa hannu ya zama doka.

“Kudurorin haraji irin wadannan suna bukatar taja da tsifa sosai. Dole bangarorin masana shari’a na zaurukan majalisun biyu su tabbatar kudurorin sun yi daidai da dokokin da ake da su a kasa kafin su tura wa Shugaban Kasa.

“Ba aiki ba ne na kwana biyu ko uku. Bayan an kammala aikin daidaita su kuma Akwun Majalisar Dokoki ta Kasa zai mayar da su kundi daya. Bayan haka ne kawai Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su sa hannu a aike da su,” in ji Sanatan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet