Featured
Mamakon Ruwa Ya Yi Ajalin Wani Matashi A Gombe

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar wani matashi da aka tsinci gawarsa a wani rami sakamakon mamakon ruwan da aka tafka a safiyar Litinin 30 ga Yuni 2025, a unguwar Hayin Kwarin Misau.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa sunn samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:30 na safe daga ofishin ‘yan sanda na Hayin Kwari, Misau, bayan gano gawar wani yaro a wani rami da ya mutu sakamakon mamakon ruwan da ya faru.
Abdullahi ya ce: “Jami’anmu sun garzaya wurin da aka ce an sami gawar, kuma binciken farko bai nuna wani alamar raunuka ko wani abu makamancin haka jikin marigayin ba.
“Muna zargin cewa mamakon ruwan da aka yi ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa.”
Da yake jawabi a yau Talata 01 ga Yuli 2025, PPRO ya bayyana cewa yaron da ake kyautata zaton yana da kimanin shekara 15, ba a samu wata shaidar da za ta nuna waye shi ko daga ina yake ba. Ya ƙara da cewa: “An ɗauki gawarsa zuwa Babban Asibitin Gombe, inda likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa.”
Ya kuma kara da cewa, tuni ‘yan sanda masu bincike suka ɗauki hotuna a wurin da aka samo gawar, inda kuma ake cigaba da bincike kan musabbabin mutuwar matashin, tare da ƙoƙarin gano ko wanene da kuma inda danginsa suke.