Featured
Manufofin Tinubu Na Tattalin Arziki Su Na Taimakawa Wajen Daidaita Darajar Naira – Dangote
Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce manufofinsa na tattalin arziki na taimakawa wajen daidaita kasuwar musayar kuɗi da kuma ƙarfafa darajar Naira.
Dangote ya bayyana hakan ne a lokacin da Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Jumoke Oduwole, ta kai ziyarar aiki zuwa Kamfanin Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals da Dangote Fertiliser Limited da ke Ibeju-Lekki, Lagos.
Ya ce gyare-gyaren da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso ya aiwatar sun taka rawar gani wurin kawo kwanciyar hankali a kasuwar canjin kuɗi.
Dangote ya kuma yaba da ƙoƙarin Shugaba Tinubu wajen magance matsalolin da ke hana wadatar danyen mai ga matatun cikin gida, yana mai bayyana shirin “Naira-for-Crude” da manufar “Nigeria First” a matsayin matakai masu ƙarfi da za su iya farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa cikin sauri fiye da yadda ake tsammani.
“Ina ganin ya kamata mu gode wa Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kokarinsa na tabbatar da cewa an samu sauki wajen samar da danyen mai.
“Matakin da ya ɗauka na cewa duk cinikayyar danyen mai za ta kasance cikin Naira abin a yaba ne ƙwarai. Domin mu iya biyan bukatun kasuwa – wanda hakan zai yiwu – dole ne a rika siyar da danyen mai cikin kuɗinmu na gida,” in ji Dangote.
Fitaccen ɗan kasuwar ya ce waɗannan matakai tare da sauran gyare-gyaren tattalin arziki sun kawo kwanciyar hankali a kasuwar kuɗi, musamman a darajar Naira da Dala. Ya bayyana fatan cewa Naira za ta ci gaba da ƙarfafa a makonni masu zuwa yayin da sakamakon gyare-gyaren ke ƙara bayyana.
“Mun fara ganin daidaito a canjin Naira da Dala, wanda hakan ya kawo fa’ida sosai. Rashin yawan sauyin darajar kuɗi ya kawo haske da kwanciyar hankali a kasuwa.
“A bangarenmu mu ‘yan kasuwa, wannan ci gaba ne mai kyau, domin yana bamu damar tsara harkokinmu yadda ya kamata. Idan yanayin kasuwa ya ci gaba da inganta, za mu ci gaba da samun darajar musaya mai fa’ida,” a cewarsa.
