Featured
Mafi Yawanci Gidajen Gyaran Hali a Najeriya Sun Haura Shekaru 100 – Ministan Harkokin Cikin Gida

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa akalla gidajen gyaran hali 12 daga cikin 246 da ake da su a Najeriya ake gyarawa a halin yanzu.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 15 ga Agusta, yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya ce da dama daga cikin gidajen gyaran halin sun haura shekara 100 da kafuwa kuma suna matuƙar buƙatar sabuntawa.
“Shugaban ƙasa bai zama shugaban ƙasa shekaru 100 da suka wuce ba. Muna da gidajen gyaran hali 246, kuma babu ɗaya da aka kafa a ƙarƙashin wannan gwamnatin.
“Wanda yake a Ikoyi, ina tsammani an kafa shi a 1956. Wanda aka yi barna a Suleja kuwa, ina tsammani an kafa shi a 1914, kuma akwai gidajen gyaran hali da dama da suka haura shekara 100.
“Zan iya faɗa muku cewa kusan gidajen gyaran hali 12 yanzu haka suna cikin aikin gyara,” in ji ministan.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin cibiyoyin ba su da likitoci har sai da Shugaba Bola Tinubu ya amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya a wuraren.
“Idan ka duba abin da wannan gwamnati ta yi cikin shekaru biyu da suka gabata, har da na Port Harcourt prison wanda ya lalace ƙwarai, da abin da Shugaban ƙasa ya yi a Kuje inda a ‘yan makonni da suka gabata aka gudanar da manyan ayyukan tiyata.
“Wannan ba kawai gina gine-gine ba ne. Lokacin da muka zo mulki, akwai jihohi da dama inda babu ko likita ɗaya a gidan gyaran hali. Amma Shugaban ƙasa ya zo, ya amince da ɗaukar likitoci 50, nas-nas 100, sannan ya amince a tura likitocin NYSC zuwa gidajen gyaran hali,” in ji Tunji-Ojo.
Kan abin da gwamnati ke yi don ƙarfafa tsaron gidajen gyaran hali, ministan ya ce, “Akwai abubuwa da dama suna gudana. Wasu abubuwa ba na son in yi cikakken bayani. Kamar yadda na ce, muna da gidajen gyaran hali 246.
“Ba za ka iya tsammanin Shugaban ƙasa ya gyara wurare 246 — kuma a kowanne wuri kana iya samun gine-gine kusan goma — cikin shekaru biyu ba. Don haka abin da muke yi shi ne haɗin gwiwa.