Featured
Gwamnatin Sokoto Ta Kashe Naira Biliyan 4.7 Wajen Yi Wa Dalibai Rajistar WAEC Da NECO a Shekaru Biyu

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce ta kashe Naira biliyan 4.7 wajen biyan kuɗin rajistar ɗalibai na jihar domin rubuta jarabawa a cikin shekaru biyu da suka wuce.
Kakakin Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, Farfesa Ahmed Ala, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da Hukumar Labarai ta Najeriya (NAN) a ranar Alhamis 14 ga Agusta a Abuja.
A cewar Farfesa Ala, jarabawar sun haɗa da ta Hukumar Jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC), Hukumar Jarabawar Ƙasa (NECO), Hukumar Shirya Shiga Jami’a (JAMB) da kuma Hukumar Kula da Karatun Fasaha (NBTE).
Ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa duk ɗaliban da suka cancanci rubuta jarabawar a jihar sun samu damar rubuta ta, ba tare da la’akari da halin kuɗin iyayensu ko masu kula da su ba.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tana kashe kusan Naira miliyan 66 wajen biyan kuɗin “imprest” ga shugabannin makarantu na sakandare, domin kula da gaggawar buƙatun makarantu kamar ƙananan ayyukan gyare-gyare.
A karkashin tsarin, kowanne shugaban makaranta yana karɓar Naira 200,000 a kowane wata daga gwamnatin jihar a matsayin “imprest”.
Haka kuma, domin ƙarfafawa malamai a jihar, gwamnati ta ƙara musu albashi daga Naira 20,000 zuwa akalla Naira 70,000, wanda shi ne mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
“Kafin zuwan wannan gwamnati, kafin malami ya samu albashinsa, kusan sai ƙarshen watan mai zuwa; shiyasa gwamnati ta tara bashi wajen albashi.
“Amma yanzu, zuwa ranar 19 ko 20 na kowane wata, duk malamai sun karɓi albashinsu, sai idan akwai jinkiri daga bankinsu,” in ji shi.
A cewarsa, gwamnatin jihar na da niyyar ƙara yawan ɗaliban da ke shiga da kuma ci gaba da kasancewa a makarantar firamare da sakandare.
Don cimma wannan, ya ce ma’aikatar tana wayar da kan iyaye da masu kula da yara kan muhimmancin ba wai kawai su saka ‘ya’yansu a makaranta ba, har ma su tabbatar da cewa sun kammala karatunsu.
(NAN)