Connect with us

Featured

INEC Ta Cigaba Da Yin Rajistar Zaɓe a Fadin Najeriya

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za a fara ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a a fadin Najeriya daga yau.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin 18 ga Agusta, hukumar ta ce ta fara da matakin rajista ta yanar gizo daga yau Litinin, 18 ga Agusta, 2025.

INEC ta bayyana cewa ‘yan Najeriya wadanda su ka cancanta za su iya fara rajistarsu ta yanar gizo a shafin www.cvr.inecnigeria.org, kafin fara rajistar kai tsaye wadda za a bude daga ranar 25 ga Agusta, 2025.

Hukumar ta ce: “Rajistar kai tsaye za ta gudana a ofisoshinmu guda 37 na jihohi da kuma a ofisoshin kananan hukumomi 774 a fadin kasa, domin saukaka wa masu kada kuri’a.”

An bayyana cewa wannan rajistar za ta kunshi:

Sabbin masu kada kuri’a masu shekara 18 zuwa sama.

Wadanda suke son karbar ko canja wurin katin zabe (PVC).

Wadanda katin zabensu ya lalace ko ya bace.

INEC ta gargadi jama’a da su guji yin rajista fiye da sau daya, inda ta ce duk wanda aka samu da hakan zai fuskanci hukunci.

Hukumar ta kuma shawarci ‘yan kasa da su yi amfani da wannan dama, saboda yin rajista na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa kowa ya samu damar shiga tsarin dimokuradiyya.

Domin karin bayani, hukumar ta ce jama’a na iya tuntubar cibiyar kiran ta a 0700-CALL-INEC (0700-2255-4632) ko ta hanyar lambar gajeriyar sako 4632.

INEC ta kara jaddada cewa tana da cikakkiyar niyyar karfafa dimokuradiyya a kasar, tare da tabbatar da cewa kowane dan kasa mai cancanta zai samu damar yin rajista kafin zabubbukan da ke tafe.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet