Connect with us

Featured

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 13 a Masallaci a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta tura karin jami’an tsaro bayan mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai, inda suka kashe mutane 13 a masallaci yayin sallar asuba a Malumfashi, a ranar Talata 1 ga Agusta, 2025.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a wani harin na ramuwar gayya da ‘yan bindigar su ka kai, sun bude wuta kan masallata a Unguwan Mantau, inda suka halaka mutane 13.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dakta Nasir Mu’azu, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa gwamnati ta dauki matakan gaggawa na karin tsaro da tallafi bayan aukuwar lamarin.

Ya ce: “Lamarin ya faru ne lokacin da miyagu suka kai harin ramuwar gayya a kauyen. Lokacin da al’ummar musulmi su ke cikin masallaci suna sallar Asuba, sai wadannan miyagun suka fara harbe-harbe cikin masallacin.

“Harin ramuwar gayya ne saboda ‘yan kauyen Unguwan Mantau sun yi kwanton bauna kwanaki biyu da suka wuce suka kashe wasu daga cikinsu. Hakan ya taimaka wajen ceto mutanen da aka sace daga kauyen Ruwan Sanyi, sannan suka kwace bindigogi AK-47 guda biyu da babura uku daga hannun ‘yan bindigar.

“Yanzu haka jami’an tsaro suna Unguwan Mantau domin dawo da zaman lafiya.

“Kwamandan rundunar sama na Forward Operating Base tare da sojojin Najeriya da ‘yan sanda sun riga sun isa wajen domin fatattakar ‘yan bindigar. Musamman a lokacin damina, ‘yan bindiga na boyewa a cikin amfanin gona domin aiwatar da miyagun ayyukansu. Mun kuduri aniyar cafke su domin fuskantar doka.

“A matsayinsu na gwamnati, muna jinjinawa jaruntaka da jajircewar mutanen Unguwan Mantau. Gwamnati za ta ci gaba da kare al’ummomi da kuma tabbatar da tsaro a ko’ina.

“Gwamnatin Jihar Katsina tana mika ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar da goyon baya ga tsare-tsaren tsaro na al’umma domin kawar da miyagu daga yankin.”

 

 

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet