Connect with us

Featured

NDLEA Ta Cafke Wani Matashi Ɗauke Da Tramadol 7,000 A Kano

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano ta ce ta cafke wani matashi dan shekara 29 da ake zargi da rike kwalaben Tramadol 7,000. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano, ranar Litinin 25 ga Agusta, 2025.

 

Ya ce an kama wanda ake zargin ne ranar Asabar a hanyar Zaria-Kano, Kwanar Dangora, ta hannun jami’an NDLEA na ofishin Kiru. Rahoton ya kara da cewa an gano kwayoyin, masu nauyin kilo 4.1, a cikin jarkar mai mai lita 20, bayan ya taho daga jihar Legas.

 

Muhammad-Maigatari ya bayyana wannan samame a matsayin gagarumin nasara wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar. Ya ce jami’an hukumar sun nuna kwarewa da jajircewa wajen gano inda aka boye haramtattun kwayoyin.

 

Shugaban hukumar NDLEA na Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, ya yaba da kokarin jami’ansa tare da godewa shugaban hukumar na kasa, Janar Manjo mai ritaya Buba-Marwa, bisa irin goyon bayan da yake bayarwa. Ya kuma nanata kudirin hukumar na kawar da miyagun kwayoyi daga jihar.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet