Connect with us

Featured

Ghana Ta Amince Da Karɓar ‘Yan Najeriya Da Aka Kora Daga Amurka

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa kasar ta fara karɓar ‘yan ƙasashen Afirka ta Yamma da Amurka ta kori, ciki har da ‘yan Najeriya. Ya ce tuni an saukar da mutane 14 na farko a Accra, waɗanda suka haɗa da ‘yan Najeriya, wani ɗan Gambiya, kuma tuni hukumomi a Ghana su ka fara taimaka musu domin komawa ƙasashensu.

Mahama ya ce Amurka ta roƙi Ghana ta karɓi waɗanda ba ‘yan ƙasar Ghana ba amma ‘yan Afirka ta Yamma, inda suka amince saboda dukkan ‘yan Afirka ta Yamma na iya shiga Ghana ba tare da biza ba. Ya ƙara da cewa, ba laifi ba ne domin “dama ba su buƙatar biza” idan za su je Ghana.

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da gwamnatin Donald Trump ke ƙara tsananta manufofinta na korar baƙin haure. A baya an yi irin wannan tsarin zuwa ƙasashen Eswatini, Sudan ta Kudu da Rwanda duk da damuwar tsaro da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam suka nuna.

Sai dai Najeriya ta ƙi amincewa da irin wannan shiri daga Amurka. Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta karɓi waɗanda ba ‘yan Najeriya ba, saboda matsalolin tsaro da tattalin arziki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet