Featured
Idan Ana Neman Inda Ake Kama-Karya A Harkar Demokaraɗiyya a Duniya To Najeriya Ne – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da aka riga aka lalata harkar dimokuraɗiyya, saboda rashin gaskiya da riƙon amana a tsakanin shugabanni. Obi ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawar dimokuraɗiyya na shekara-shekara da Gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a birnin Accra, Ghana, mai taken “Me Ke Kashe Dimokuraɗiyya?”
Obi ya ce dimokuraɗiyya ba ta da amfani matukar ba za ta amfani alumma, kuma za ta daina fifita bukatun al’umma, sannan kuma ta gaza bayar da ilimi, kiwon lafiya da tsaro ga ‘yan ƙasa. Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya na buƙatar shugabanni masu gaskiya, cancanta da kishin al’umma, ba don son kai ko aljihu ba.
Ya kuma zargi yadda dimokuraɗiyyar Nijeriya ta zama hanyar da wasu ‘yan tsiraru ke shiga gwamnati don amfanin kansu da na iyalansu. Obi ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su mayar da hankali a lokacin zaɓe wajen zaɓar shugabanni masu cancanta, nagarta da tausayi.
A wani bangare na jawabin nasa, Obi ya soki dokar ta-baci ta watanni shida da aka janye a Jihar Rivers a ranar Laraba, 17 ga Satumba, yana mai kiran hakan “kuruciyar doka” da kuma barna ga dimokuraɗiyya. Ya ce ya kamata ya yi a koyi darasi daga irin wannan lamari don ci gaban dimokuraɗiyyar Nijeriya.