Connect with us

Featured

Tsare-tsaren Da Mu Ka Kawo A Fanni Ilimi Shi Ne Ya Sa Ɗaliban Kano Su Ka Yi Zarra a Jarabawar NECO – Gwamnan Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa nasarar da jihar ta samu a jarabawar kammala sakandare ta NECO na shekarar 2025 ta samo asali ne daga tsare-tsaren sauye-sauye da gwamnatin sa ta aiwatar a fannin ilimi. A cewar gwamnan, wannan nasara ba ta zo ta hanyar bazata ba, illa sakamakon jajircewar gwamnati wajen mayar da ilimi sama da komai a cikin manufofinta.

Rahoton NECO ya nuna cewa Kano ta fi kowace jiha a yawan daliban da suka samu sakamako mai kyau, inda dalibai 68,159 suka samu ƙididdigar sakamako mai kyau ciki har da Ingilishi da Lissafi – wanda ke wakiltar kashi 5.02 cikin ɗari na ƙasa baki ɗaya. Lagos ce ta biyo bayan da ta samu dalibai 67,007, sai Oyo wadda ta samu 48,742.

Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin sa ta bai wa ilimi kaso mafi tsoka a kasafin kudin shekarun 2024 da 2025, abin da ya sa aka samu damar aiwatar da muhimman gyare-gyare. Ya jero irin matakan da aka ɗauka da suka haɗa da rabon kayan makaranta kyauta, gyaran ajujuwa, ɗaukar sabbin malamai tare da horas da su, ƙarin tallafin kuɗi ga cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare, da kuma shirye-shiryen tallafin karatu ga ‘yan asalin Kano.

Haka zalika, gwamnan ya ce an ba da muhimmanci ga ilimin ‘ya’ya mata tare da rage yawan yara marasa zuwa makaranta. Ya jaddada cewa wannan nasara hujja ce da ke nuna cewa gwamnati na kan hanya madaidaiciya, tare da tabbatar da cewa babu yaro ko yarinya a Kano da za a bari a baya a sha’anin ilimi.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet