Connect with us

Featured

Gwamna Abba Kabir Yusuf Zai Koma APC Ranar Litinin – Sanusi Bature

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai koma jam’iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026, bayan ya ajiye mukaminsa daga jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta tuna cewa Gwamna Yusuf ya fara shiga APC ne a 2014, inda ya lashe zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, wadda daga bisani ya mika wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ta ce bayan shafe shekaru yana fafutukar siyasa a jam’iyyu daban-daban, halin da ake ciki na shugabanci, haɗin kan ƙasa da ci gaba ne suka sa ya yanke shawarar komawa APC.

Gwamnan ya ce komawarsa APC za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, ta hanzarta bunƙasa ababen more rayuwa, inganta tsaro da kuma hidima ga al’ummar Kano. A ranar Litinin ɗin, zai yi rijista a APC tare da ’yan Majalisar Dokokin Jiha 22, ’yan Majalisar Wakilai takwas da shugabannin ƙananan hukumomi 44, tare da ƙaddamar da shirin rijistar APC ta intanet a jihar.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet