Connect with us

Featured

Gwamnan Kano Ya Yi Alƙawarin Kawo Ƙarshen Jinkirin Biyan Haƙƙoƙin Ma’aikatan Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta ƙara lamunta jinkiri wajen biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati ba, yana mai cewa duk wanda ya yi wa al’umma hidima ya cancanci a biya shi hakkinsa ba tare da ɓata lokaci ba. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Tofa, ya fitar a ranar Alhamis, 18 ga Disamba 2025 da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin rabon alawus-alawus na barin aiki, na masauki da na hutun aiki ga tsofaffin kansiloli 1,371 da suka yi aiki tsakanin 2021 zuwa 2024, a Coronation Hall na Fadar Gwamnati da ke Kano. A cewarsa, an raba jimillar Naira biliyan 8.26, wanda ke nuni da kammala dukkan bashin da ake bin tsofaffin kansilolin, inda wasu suka karɓi kuɗaɗe tsakanin Naira miliyan 5 zuwa 6 kai tsaye.

 

Gwamna Abba Yusuf ya ce wannan mataki wani bangare ne na gyare-gyaren da gwamnatinsa ke yi domin hana tara bashin haƙƙoƙin ma’aikata a nan gaba, tare da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati. Rahoton Kakaki24 ya nuna cewa gwamnan ya kuma bukaci al’ummar Kano da su mara wa gwamnatinsa baya wajen gina jiha mai adalci da walwala, yana mai jaddada cewa girmama sadaukarwar ma’aikata shi ne ginshiƙin ingantacciyar mulki.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet